UMSHIYA
Taken bincike i
Tabbatarwa ii
Sadaukarwa iii
Godiya iv
Umshiya vii
BABI NA DAYA: GABATARWA
1.0 Shimfi]a 1
1.1 Bitar Ayyukan Da Suka Gabata 3
1.2 Hujjar Ci Gaba Da Bincike 8
1.3 Hanyoyin Gudanar Da Bincike 11
1.4 Muhalin Bincike 12
1.5 Manufofin Bincike 12
1.6 Na]ewa 13
BABI NA BIYU: TAKAITACCEN TARIHIN ‘YARKASUWA
2.0 Shimfi]a 15
2.1 Tarihin Garin Sifawa A Takaice 16
2.2 Ma’anar ‘Yarkasuwa 19
2.3 Dalilin Zuwan Su Cin Kasuwar 21
2.4 Garuruwa Ko Kauyukan Da Ke Cin ‘Yarkasuwa 22
2.5 Na]ewa 23
BABI NA UKU: NAU’O’IN KAYANDA A KE SAYA DA
SAYARWA A ‘YAR KASUWA
3.0 Shimfi]a 25
3.1 Kayan Abinci 26
3.1.1 Shinkafa 26
3.1.2 Gero 27
3.1.3 Masara 27
3.1.4 Dawa 28
3.1.5 Maiwa 28
3.1.6 Hatsi/Damma 29
3.1.7 Wake 29
3.1.3 Gya]a 30
3.2 Kayan Miya 30
3.2.1 Tumatur 31
3.2.2 Tattasai 31
3.2.3 Tarugu 31
3.2.4 Albasa 32
3.2.5 Alayyahu 32
3.2.6 Sure 32
3.2.7 Kabushi/Kabewa 33
3.3 Kayan Marmari 33
3.3.1 Ayaba 34
3.3.2 Lemun Yami 34
3.3.3 Lemun Zaki 35
3.3.4 Karas 35
3.4 Dabbobi 35
3.4.1 Shanu 36
3.4.2 Raguna 36
3.4.3 Akuyoyi 37
3.4.4 Kaji 37
3.5 Sutura 37
3.5.1 Shaddodi 38
3.5.2 Atamfa 38
3.6 Sana’o’in Da Suka Yi Fice A Kasuwar 39
3.6.1 Sana’ar Sayarda Nama (Rundawa) 39
3.6.2 Kayan Gwari (Kayan Miya) 39
3.6.3 Sana’ar Sakai 40
3.6.4 Sana’ar Shayi Da Burodi 40
3.7 Na]ewa 41
BABI NA HU[U:
TASIRIN KASUWAR ‘YAR KASUWA A GARIN SIFAWA
4.0 Shimfi]a 43
4.1 Amfani Da Ake Samu A Cikin Kasuwar 44
4.1.1 Ana Shigowa Da Abubuwan Da Ba Bu Su A Cikin Kasuwar Garin 44
4.1.2 Matasa Suna Samun Aikin Yi A Cikin Kasuwar 45
4.1.3 Ci Gaban Garin Sifawa 45
4.2 Matsalolin ‘Yar Kasuwa 46
4.2.1 Rashin Wutar Nepa (Lantarki) 46
4.2.2 Rashin Tallafi Daga Gwamnati 47
4.2.3 Rashin Ruwan Fanfo 47
4.2.4 Rashin Ofishin Yan Sanda A Cikin Kasuwar 48
4.3 Na]ewa 48
BABI NA BIYAR
TA{AITAWA DA KAMMALAWA
5.0 Shimfi]a 50
5.1 Ta}aitawa 50
5.2 Kammalawa 53
Manazarta 56
BABI NA DAYA:
GABATARWA
1.0 SHIMFI[A
Sha’a nin kasuwanci sha’ani ne mai matu}ar muhimmancin gaske ga rayuwar al’ummar Hausawa baki ]aya. Ita kuwa kasuwa muhalli ne da ake saye da sayarwa domin biyan wasu bukatoci na rayuwar yau da kullum. Wannan bincike mai taken “Tasirin ‘Yar Kasuwa ga Al’ummar Hausawan Sifawa”. Za a yi }o}arin bayanin irin rawar da ‘yar kasuwa ta taka wurin bun}asa tattali arziki al’ummar Hausawa a garin Sifawa.
A }o}arin cimma manufar wannan aiki, an kasa aikin zuwa manya-manyan sassa (babi) guda biyar domin samun saukin aikin kamar haka. A babi na farko mai suna gabatarwa yana da }ananan sassa guda shida, wa]anda suka ha]a da sashe mai lamba 1.0 Gabatarwa da 1.1 Bitar ayyukkan da suka gabata da 1.2 Hujjar ci gaba da bincike da 1.3 Hanyoyin gudanar da bincike da 1.4 Muhallin bincike, da 1.5 Manufar bincike sai 1.6 Na]ewa.
A babi na biyu kuwa mai suna “Ta}aitaccen Tarihin ‘Yar kasuwa”. A nan babi na da }anana sassa guda hu]u wa]anda suka ha]a da 2.0 Shimi]a da 2.1 Tarihin garin Sifawa a ta}aice da 2.2 da 2.3 Garuruwan da ke cin kasuwar sai kuma 2.4 Na]ewa.
A babi na uku kuma mai taken nau’o’in kayan da ake saya da sayarwa a ‘yar kasuwa. Wannan babi an kasa shi zuwa babi shida kamar haka: 3.0 Shimfi]a sai 3.1 kayan abinci a ‘yar kasuwa, da 3.2 kayan miya a ‘yar kasuwa sai 3.3 kayan marmari a ‘yar kasuwa da kuma 3.4 dabbobi ‘yar kasuwa, da 3.5 sutura ‘yar kasuwa. Sai kuma sashen }arshe wanda ya yi bayanin kayan da aka fi samu a cikin ‘yar kasuwa ke nan 3.6 sai 3.6.5 na]ewa.
Bayan haka akwai babi na hu]u wanda ake masa suna “Tasirin kasuwar ‘yar kasuwa a garin Sifawa” shi wannan babi an kasa shi zuwa sassa daban-daban a cikin babin. Na farko 4.0 Shimfi]a, sai kuma 4.1 amfanin da ake samu a cikin kasuwa‘yar kasuwa 4.1 shigowa da abubuwan da babu su a cikin kasuwar garin, 4.1.2 matasa suna samun aikin yi a cikin kasuwar garin, 4.1.3 ci gaban garin Sifawa baki ]aya.
4.2 matsalolin ‘yar kasuwa, 4.2.1 rashin wutar lantarki (NEPA), 4.2.2 rashin tallafi daga gwamnati, 4.2.3 rashin ofishin ‘yan sanda a cikin kasuwar, 4.2.5 Na]ewa. Sai babi na biyar wannan sashen ya nada sashe har hu]u a cikinsa. 5.0 Shimfi]a 5.1 Ta}aitawa, 5.2 Sakamakon bincike, sai 5.3 Kammalawa.
1.1 BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA
Har wa yau a cikin wannan aiki za a ta~o wasu aikace-aikace da suka gabata masu dangantaka dangane da wannan bincike wato harakar kasuwanci a cikin ‘yar kasuwa ta garin Sifawa. A ha}i}anin gaskiya an ]an yi wasu ayukka wa]anda suka danganci wannan fanni, amma sun sha banban da wannan. Saboda a cikin bincike binciken da na yi na ci karo da wasu kundaye na digiri wa]anda aka gabatar makamantan wannan aiki kuma sun taimaka wajen assasa wannan bincike.
Bincike na farko da aka duba na wani ]alibi mai suna Umar M.
(2005). A cikin aikinsa mai taken “Kasuwanci muhimmancinsa ga al’umma Hausawa”. A kundin digirinsa na farko. A sashen nazarin harsunan Nijeriya na Jami’ar Usmanu [anfodiyo ta Sakkwato. Wnanan ]alibi ya dubi wane ne ]an kasuwa da kuma ma’anar kasuwanci a al’umma. Bayan haka ya dubi irin kayan da ake sayarwa a cikin kasuwa da huldayyar da Hausawa ke yi da wasu al’ummomi daban-daban. Ya kuma dubi matsayin kasuwanci a yau.
Bugu da }ari ya kawo dangantakar kasuwanci da al’ada inda ya dubi wasu sana’o’in Hausawa da ake samu a cikin kasuwanni da kuma yadda ake aiwatar da su a cikin kasuwanni.
Bayan haka wannan ]alibi ya dubi kasuwanci da kuma bun}asarsa ga al’umma, a nan idan aka dubi aikin wannan ]alibi ya so ya yi kama da wannan domin ya kawo ire-iren abubuwan da ake sayarwa a cikin kasuwa da ma’anar kasuwa, da hul]ayyar da Hausawa ke yi da wasu al’ummomi daban-daban da sauransu. Don haka, aikin ya banbanta da wannan aikin domin an mai da hankali ne ga tasirin ‘yar kasuwa a al’ummar garin Sifawa ne a wannan bincike. Bayan haka, bincike na biyu da aka yi na wani ]alibi mai suna
Gali (1986). A cikin aikinsa mai suna “KASUWANCI DA DA NA YANZU A BIRNIN KANO”. A kundin digiri na farko, a Sashen Nazarin Harsuna Najeriya na Jami’ar Usmanu [anfodiyo ta
Sakkwato. A cikin aikinsa ]alibin ya dubi tsarin cikin birnin Kano ya kuma kawo yadda ake fara yin kasuwanci a cikin birnin Kano da kuma fataken da suke shigowa a cikin birnin Kano don su yi kasuwanci wa]anda aka bar yayinsu wato sun tsufa ambarcinsu misali; Kasuwar Sabon Gari, Kasuwar Kwari. Bayan haka, ya kawo sababbin kasuwani da suke tashi a birnin na Kano, kamar Kasuwar
}ofar Wanbai, Kasuwar }ofar Ruwa, sai Kasuwar }ofar Na’isa da kuma Kasuwar ‘Yar Kaba.
Bayan haka, ]alibin ya yi }o}arin kawo wasu sana’o’in da ake yi kamar irinsu }ira, jima, dukanci, da kuma rini. Ya kawo tarihin zuwan Turawa tare da shigowar kasuwanci a birnin na Kano. Abin lura a nan, wannan aikin na wannan ]alibi yana da alaka da nawa domin ]alibin ya kawo tarihin birnin Kano har lokacin da turawa suka zo suka fara yin kasuwanci. Wannan ya }ara mani }arfin guiwa ya sa na yi bincike na kafuwar ‘yar kasuwa a garin Sifawa. Don haka ayyukan namu sun yi kama domin duk suna magana ne a kan kasuwanci daga wani sashen }asar Hausa.
Bugu da }ari, an yi bitar bincike na wani ]alibi mai suna Bello (2004). A cikin aikin sa mai suna “NAZARI A KAN KASUWAR KARA TA SAKKWATO. A cikin kundin digirinsa na farko, a Sashen Nazarin Harsunan Najeriya na Jami’ar Usmanu [anfodiyo ta Sakkwato. A cikin wannan aikin na wannan ]alibi, ya yi }o}arin kawo ma’anar kasuwanci da kuma yadda ma’anar kara ta samo asali da kuma kasuwanci dabbobi da ire-iren dabobin da ake sayarwa a cikin kasuwa ‘yar kasuwa ta kara. Bayan haka, ]alibin ya yo tsokaci kan muhimmancin kasuwar kara a cikin al’umma da shuwagabanninta, ya kuma dubi irin ba}in mutanen da suke kawo dabbobi a cikin kasuwar domin su sayar da su.
Wa]annan ba}i sun ha]a da mutanen Nijar da mutanen Kebbi. [alibin ya yi }o}arin kawo ta}aitaccen tarihin birnin Sakkwato. Wannan aikin na wannan ]alibi ya so ya yi kama da nawa domin mun yi tarayya wajen kawo tarihin gari da abubuwan da ake samu a cikin kasuwa da take ci, da sauransu. Sai dai shi yana magana ne a kan kasuwar kara, wannan aikin kuwa yana nazari ne a kan kasuwar ‘yar kasuwa ta garin Sifawa.
Bayan haka, wani bincike da na yi bita shi ne na wani ]alibi mai suna Aliyu (2011). A cikin aikin sa mai taken: “HARSHEN KASUWANCI NA GIDA DA NA BAKI A KASUWAR, ALBASA TA ALERU”. A kundin digirinsa na farko a }ar}ashin Sashen Nazairn Harsunan Najeirya na Jami’ar Usmanu [anfodiyo ta Sakkwato. [alibin ya kawo ma’anar kasuwanci da kawo tarihin kasuwancin Bahaushe da kuma muhimmanci kasuwanci ga al’umma. [alibin ya kawo ha~akar tattalin arzikin }asa. Bayan haka ya kawo cewa, kasuwanci kariya ne daga zaman kashe wando ya yi tsokaci kan wasu karuruwan harshe da ake samu sanadiyar kasuwanci. Ya kuma ce, kasuwanci yana raya }auyuka har ma da birane, ya kuma kawo ta}aitaccen tarihin garin Aleru da kuma kasuwar albasa da ke garin na Aleru. Bugu da }ari ya kawo yanayin kasuwanci a }asar ta Aleru, da }ir}irar sababbin kalmomi a cikin harshen kasuwanci gida da na ba}i ya kawo dalilin samuwar sababbin kalmom a harshen kasuwanci harwa yau ]alibin ya kawo nau’o’in kalmomin }ir}ira a harshen kasuwanci da kuma muhimmancin }ir}irarrun kalmomi wajen harshen kasuwanci. Idan muka dubi aikin wannan ]alibi suna da kama da nawa wajen kawo tarihin gairn da kasuwar albasa da ke Aleru da ma’anar kasuwanci da kuma alfaninsa ga al’umma. Sai dai inda muka sha ban-ban da shi ni zan yi maganar ne kawai kan ‘yar kasuwa a garin Sifawa, amma duk ayukkan namu su na da kama da juna domin suna magana ne a kan kasuwanci.
Har wa yau, akwai wasu ]alibai da suka yi wani bincike a kan “HAUSAR WASU KEBABBAN SANA’O’IN HAUSAWA KULI DA AWO”. Wa]annan ]alibai sun ha]a da Adamu Zakari da Muhammad Argungu (2010). A kundin digirinsu na farko a Jami’ar Usmanu [anfodiyo ta Sakkwato. A cikin aikin wa]annan ]alibai sun yi }o}arin kawo ma’anar sana’a da kasuwanci da tarihin samuwar sana’a bayan haka sun yi }o}arin kawo ire-iren sana’o’in Hausawa.
1.2 HUJJAR CI GABA DA BINCIKE
Ko shakka babu akwai hujjoji masu karfi da suka bani }arfin gwiwar wannan bincike.
Da farko dai dukkan ayyukan da na yi bita ba su ce komai game da ‘yar kasuwa ta garin Sifawa ba, duk da yake wasu daga cikin ayyukan da aka yi bita sun shafi al’amurran saye da sayarwa ne waton kasuwanci a wasu sassan }asar Hausa. Misali aikin Umar (2005), ya yi bincike ne a kan “Kasuwanci da muhimmancinsa ga al’ummar Hausawa”. Aikin bai ce komai ba game da ‘yar kasuwa ta garin Sifawa ba, don haka ya zama hujja a kan aiwatar da wannan aikin.
Haka shi ma aikin Gali (1986), ya yi bayani kasuwanci da ake a da, a wasu kasuwanni Birnin Kano da kuma wa]anda ake cinsu a yau. Haka ya yi bayani irin nau’in kayan da ake sayarwa da kuma masu zuwa cin kasuwar da sauransu. Rashin cewa komai game da ‘yar kasuwar Sifawa ya zama hujja ga ci gaban wannan bincike. Har wa yau wani bincike wanda wani ]alibi ya mai suna Aliyu (2011). Wannan ]alibi ya yi bayani ne kawai dangane da “Harshen kasuwanci na gida da na ba}i a kasuwar Albasa wadda ke Aleru”. Inda ya yi bayanin yadda ake samun sa~abbin wasu harsuna da ake yin kasuwanci. Hujjar ci gaba da bincike shi ne bai ta~a tasirin ‘yar kasuwa wanda take garin Sifawa ba da irin ci gaban da ta samun da nau’in irin abubuwan da ake samu a cikinta, ta gefen kayan abinci da kayan marmari da sauransu ba.
Wata hujja kuwa idan aka kalli aikin Adamu da Muhammad Argungu, mai taken “Hausar wasu ke~a~~an sana’o’in Hausawa kuli da awo”. Wa]annan ]alibai sun yi bayani ne kawai a kan waus kebatattun wasu sana’o’in Hausawa wanda ya shafi ‘yar kasuwa ba da sana’o’in da ake yi a cikin ‘yar kasuwa da ke garin Sifawa.
Bayan haka, sun kawo yadda ake sarrafa yin }uli-}uli da kuma kawo yadda masu sayar da }uli-}uli suke maganarsu. Sun kawo ma’anar awo da yadda ake yinsa. Wannan aikin na wa]annan ]alibai yana da ala}a da nawa domin sun tabo ire-iren wasu sana’o’in
Hausawa sai dai wannan aikin ya ke~anta ne kawai a ‘yar kasuwar da ke garin Sifawa wanda ba su yi magana a kansa ba rashin yin haka, ya zama hujjar aiwatar da wannan bincike.
Akwai wani ]alibi mai suna Aliyu Gada (1989). A cikin aikin sa mai suna “SANA’AR SA{AR KABA A {ASAR HAUSA”. A cikin kun]in digirinsa a sashen Nazarin harsunan Najeirya na Jami’ar Usmanu [anfodiyo ta Sakkwato. Wannan ]alibin ya yi }o}arin kawo ]aya daga cikin sana’o’in Hausawa, ya kawo ]an ta}aitaccen tarihin Hausawa, da kawo ma’anar sana’ar da muhimmancin ta ga al’umma da ita kanta sana’ar kaba da irin kar~uwar da ta samu a al’ummar Hausawa, da dangantakar sana’ar kaba da sauran wasu sana’o’in.
Ya kawo muhimmancin kasuwanci ga al’umma da kawo wasu sana’o’in Hausawa a Sakkwato. Bayan haka, ya kawo ire-iren kasuwanci ga al’ummar Hausawa Kamar Fatauci da Noma, da {ira, da Jima da sauransu.
Wannan aikin na wannan ]alibi ya sha banban da nawa domin a wannan aiki ya ke~anta ne kawai a ‘yar kasuwar garin Sifawa da kuma irin abubuwan da ake samu a cikin ‘yar kasuwa da ke garin na Sifawa da irin ci gaban da ta samu da matsalolin da ke damunta duk an tabo su a cikin wannan aikin.
1.3 HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE
Kowane irin bincike da za a gudanar dole a samu hanyoyi na musamman da ya kamata a bi domin cimma nasarar gudanar da wannan bincike. Don haka, a }o}arin gudanar da wannan binciken an yi amfnai da hanyoyi da dama kamar haka.
An yi amfani da mayan kundayen digiri domin tattaro bayanai masu dangantaka da wannan aikin bincike da ke cikin dangane da kasuwanci bayan haka an yi amfani da littattafai da aka wallafa dama wa]anda ba a wallafa ba, domin tattaro bayanai. Har wa yau, kuma an yi amfani da dubarun yin tambayoyi, daga cikin wa]anda ake yi wa tambayoyin akwai dattijai da wasu ‘yan kasuwar garin
Sifawa. Bayan haka, akwai bu}atar da ta sanya aka duba mujallu da }asidu da jaridu uwa uba kuma tambayar malammai da dai sauran wasu al’umma da suka da ce a tambaya da duk domin zakulo bayanai masu muhimmanci da shawarwari domin cimma nasarar wannan aiki bincike.
1.4 MUHALIN BINCIKE
A gaskiya dai “ko mai na da iya ka amma banda ikon Allah”. Dan haka, ya zama dole a bayyana iyakar farfajiyar wannan aiki, domin haka ne za a iya bada haske ga mai karatu saboda ya iya fahintar inda aka nufa. Wannan bincike fa]insa bai wuce yadda aka ambato ba a tun can farko cewa tasirin ‘yar kasuwa a garin Sifawa. Abin da za a yi a cikin wannan aiki ba zai wuce wa]annan iyakoki ba wa]anda aka ambata ba.
A ta}aice dai farfajiyar wannan aiki ya tsaya ne kurum ga abinda ya shafi kasuwar ‘yar kasuwa a garin Sifawa. A nan aikin zai yi tsokaci ne a kan tasirinta kayan kasuwancinta, masu cin kasuwar da kuma tasirinta ga al’ummar Sifawa baki ]aya. Don haka aikin bai shafi wasu abubuwa da suke wajen wannan kunshiya ba.
1.5 MANUFOFIN BINCIKE
Kowane ilmi bincike yana da manufar aiwatar da shi, wannan aikin yana da manufofi kamar haka: Manufar farko ita ce: “shi ne duk ]alibin da zai kammala karatunsa na farko wato digiri na farko. To dole ya yi wani aiki ko bincike kafin a ba shi wannan takarda ta cewa ya kammala digiri wato B.A Hausa. Don haka, cika }a’idar da jami’a ta gindaya kafin bayar da digiri yana daga cikin manufar wannan bincike. Bayan haka, manufa ta biyu ita ce domin kawo irin ci gaban da ‘yar kasuwa ta garin Sifawa ta samu wurin ci gaban al’ummar Sifawa musamman Hausawa.
Haka kuma, binciken zai taimakawa a samu abin karantarwa da kuma yin nazari harshen Hausa. Haka manufar wannan bincike shi ne za baska hanya ga ]alibai masu sha’awar wannan fanni ta yadda za su aza nasu harsahen binciken na gaba domin za}ulo wasu abubuwa.
1.6 NA[EWA
A wannan }aramin sashe mai suna na]ewa mai lamba 1.6, a nan sashen ya yi }o}arin kawo kumshiyar aikin da aka tattauna a cikin babin ne a ta}aice. Babin yana da }ananan sassa guda shida (6) wato daga 1.0 zuwa 1.6. A sashen 1.0 yana da shimfi]a, a nan sashen ya yi bayani kumshiyar babi ne ata}aice. A sashe mai lamba 1.1 ya yi bayanin bitar ayyukan da suka gabata, wannan sashen ya yi bitar wasu ayyukan da ke da danganta da wannan aikin. A sashe mai lamba 1.2 kuma yana da taken Hujjar Ci gaba da Bincike. A nan sashen ya yi bayanin irin dalilin da suka sanya za a ci gaba da gabatar da wannan bincike. A sashe mai lamba 1.3 kuma mai taken hanyoyin gudanar da bincike, a nan sashen ya yi byanin irin dubarun da aka bi wurin gudanar da wannan bincike wa]anda suka ha]a da amfani da kundayen da littafai da ziyarce-ziyarce gidajen tarihi da tambayoyi da sauransu.
A sashe mai lamba 1.4 kuma mai suna Muhimmancin bincike, sashen ya yi bayani farfajiyar wannan bincike ne inda ya ta}aita bakin iyakar fa]in abinda za a tattaro a cikin aikin baki ]ayansa. A }aramin sashe mai lamba 1.5 kuma mai suna manufofin bincike a nan sashe ya yi }o}arin bayanin manufofin da suka sanya ake aiwatar da aikin bincike (Dalilin Bincike). A }arshe na]ewa mai lamba 1.6. A nan an yi }o}arin kawo kumshiyar babin amma a taaice.
Login To Comment